Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin ƙara wa ma’aikatan shari’a na ƙasar albashi.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yau Juma’a a jihar Rivers, yayin ƙaddamar da sabon ginin makarantar horas da lauyoyi da ke jihar.
Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, wanda shi ne ya wakilci shugaban ƙasar, ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙarin inganta albashin ma’aikatan shari’ar ne domin ƙarfafa ɓangaren da kuma tabbatar da ƴancinsa.
Ya ce yanzu haka shugaba Buhari ya umurci shugaban hukumar tarawa da raba kuɗaɗen haraji na ƙasar, da ministan sharia’a su ɗauki matakan ganin an fara aiwatar da ƙarin albashin.
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 20 hours 42 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 22 hours 23 minutes 56 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com