Rahotannin na bayyana cewa ministan matasa da wasannin na Nijeriya Sunday Dare ya tabbatar da tsige darakta janar na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC birgidiya janar Muhammad Fadah
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa a daren juma’a domin tabbatar da sakon tambayar da aka yi masa kan gaskiyar labarin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Tunda fari da jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sallami Shugaban Hukumar kula da Matasa Ƴan yi wa ƙasa Hidima, NYSC, Muhammad Kukah Fadah, ƙasa da watanni 6 da naɗa shi.
Kawo yanzu dai babu wani dalili da a ka bayyana cewa shi ne ya sanya Buhari ya sallami Fadah, amma wata nahiyar sirri a fadar shugaban ƙasa ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa korar ta sa ba ta rasa nasaba da rashin ƙoƙari tun bayan da ya kama aiki.
Sai dai kuma PRNigeria ta ruwaito cewa tuni a ka baiwa Fadah umarnin ya mika ragamar aiki ga ma’aikaci mafi matsayi a hukumar wanda zai zama shugaban na riƙo.












