Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta kubutar da Tsoho dan Shekara 75 daga hannun ‘Yan Ta’adda

Rundunar ‘yan sanda jihar zamfara ta sami nasarar kubutar da wani tsoho mai kimanin shekaru 75 daga hannun ‘yan Ta’adda a jihar.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar SP Mohammed Shehu Anipr, a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Kolo Yusuf psc.
Sanarwar tace rundunar a ranar Juma’a ta sami nasarar kubutar da tsohon mai suna Muhammad Shehi dan asalin garin Enagi a karamar hukumar Edati ta jihar Niger, bayan ya kwashe watanni a hannun ‘yan bindigar.
Dakarun rundunar sun gudanar da atisayen ne bayan samun wani rahoton sirri kan sace tsohon, nan suka shiga aiki ba dare ba rana har sai da suka sami nasarar kubutar da shi.
Tsohon ya bayyana wa jami’an cewa wasu gungun ‘yan ta’adda da suka tare hanyar birnin Gwari zuwa Kaduna a farkon watan Oktoban 2022, suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji a wani yanki na dan sadau dake jihar ta Zamfara, inda ya kwashe watanni 2 a hannun su.
Sanarwa tace Likitocin sun gudanar da binciken lafiyar sa kafin Jami’an ‘yan sandan su sadashi da iyalen sa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya taya ‘yan uwa da iyalen Muhammad murna bisa samun dan uwan su da suka yi daga bisani ya tabbatar da kudirin hukumar na kare lafiya da dokiyoyin Al’umma

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 12 hours 2 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 43 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com