Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bai wa kamfanin man NNPC da kungiyar dalilan man fetur ta IPMAN wa’adin sa’o’i 48 su tabbatar da wadatuwar fetur a fadin kasar.
Read Also:
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Kakakin hukuma, Peter Afunanya, ya fitar a Abuja bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkokin fetur.
Sanarwar ta ce NNPC ta tabbatar da cewa tana da wadataccen fetur jibge da zai wadatar da ‘yan kasar har bayan bukukuwa karshen shekara.
Ya ce an baza jami’an DSS a kowacce kusurwa ta kasar domin hukunta duk maso boye mai ko yiwa harkar samar da mai zagon-kasa.