Home DUNIYA Babu Gudu ba Ja Da Baya Kan Sabon Tsarin Takaita Cire Kudi...

Babu Gudu ba Ja Da Baya Kan Sabon Tsarin Takaita Cire Kudi – Godwin Emefiele

Babban bankin Najeriya, ya ce babu fashi kan sabon tsarinsa na takaitawa ɗaidaikun mutane cire kudi daga bankuna bayan kiraye-kiraye daga ko’ina a Najeriya cewar ya sake duba batun.

Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya Alhamis bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce batun da bankin zai sake dubawa shine adadin kudin da za a iya cirewa ba wai ya canja tsarin ba, inda ya ce sabon tsarin na nan daram.

Gwamnan babban bankin na magana ne bayan da majalisar wakilai ta nemi da a soke tsarin da kuma gayyatarsa zuwa gabanta domin ya yi mata bayani.

“Ina sane da batun jin karin bayani da ‘yan majalisa suka nema. Amma ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne cewa tsarin ya faro ne tun a shekara ta 2012,” in ji Emefiele.

“Sai dai kusan sau uku zuwa hudu muna soke tsarin saboda muna ganin ya kamata mu yi kyakkyawan shiri da sake gyara tsarin biyan kudi a Najeriya.

”Tsakanin 2012 zuwa 2022, kusan shekara goma kenan, muna da yakinin cewa an samar da cibiyoyi na taimakawa mutane da dama yin hada-hadar kudaɗe a fadin kasa.

Emefiele ya ce akwai tsari da za a yi wa al’ummomi a karkara don tabbatar da cewa sabbin tsare-tsare ba su yi mummunan tasiri a kansu ba.

A ranar Talata ne, CBN ya taƙaita yawan kuɗade laƙadan da ƴan ƙasar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki, inda yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp