Mamallaki kuma Wanda ya sama da Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nigeria wato (MAUUN) Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bukacin yin hadin Gwiwa da cibiyar PRNigeria domin horas da daliban Jami’ar sanin makamar aiki.
Farfesa Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin da babban Shugaban kamfanin dillancin labarai na Image Merchants Promotion Limited masu wallafa jaridun PRNigeria da Economic Confidential, Malam Yushau Shuaib, ya jagoranci tawagar kamfani Wata ziyara a jihar Kano.
Farfesa Gwarzo ya godewa shugaban Kamfanin na IMPR bisa yadda ya bashi gudunmawar shawarwari, kalaman karin karfin Gwiwa wanda suka tallafa wajen cigaban Jami’ar.
PRNigeria na matsayin wata cibiya da ta dauki shekaru tana horas da dalibai musamman na tsangayar koyon aikin Jarida daga Jami’oi mabambanta.
Alhaji Shuaib ya bawa mamallakin Jami’ar tabbacin cewa cibiyar zata bawa Daliban makarantar horarwa mai inganci kuma matakin farko a fadin duniya.
Daga bisa Shuaib ya yaba da kokarin Gwarzo bisa tallafinsa ba ganin an kammala taron bada lambar karrama matasan Arewa mai lakabin Arewa 30 Under 30 Award wanda ya gudana a makon daya gabata.
Haka zalika ya yaba da kokarin gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo bisa yadda take bada tallafin jin kai ga masu karamin karfi a cikin Nijeriya dama sauran kasashen.
Farfesa Gwarzo, wanda ya samar da Jami’oin MAUUN a Nijeriya da Nijar, yanzu haka yana shirye -shiryen samar da wasu Jami’in Franco British International University a jihar Kaduna da Canadian University a birnin Abuja cikin shekarun 2023/2024.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 27 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 8 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com