Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bada umarnin bude gadar domin yin amfani da ita na tsawon wata guda farawa da daren Alhamis.
Ministan Ayyuka Babatunde Fashola SAN, ne ya bayyana hakan yayin da yake kaddamar da gadar don amfani da ita wajen bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
Fasola a lokacin dake tafiya kan gadar ya bukaci matuka da suyi amfani da ita yadda ya kamata cikin nutsuwa kada suyi abinda zasu kawo tsaiko ga musabbabin samar da ita.
Ministan yace dalilin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kammala aiki shine domin tseratar da rayukan Al’umma da kuma kawar da talauci wanda ke aukuwa sakamakon bata sa’oi cikin cunkoso akan tsohuwar gadar Farko ta Niger.
Ya kuma tabbatar da cewa samar da gadar zai taimaka wajen rage wahalhalun da matuka ke sha cikin cunkosu a yayin bukukuwan na kirsimeti da karshen shekara.
Yace gadar bazata zama mai amfani ba muddi ba’a bi da ita yadda ya kamata ba.
Daga bisani Fasola ya ce an bude gadar a hukumance daga rana
Alhamis 15 ga Disambar 2022 da misalin 12:01am zuwa 15 ga watan Janairun 2023
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 9 hours 25 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 7 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com