Home General ‘Yan sanda sun sami nasarar halaka ‘yan ta’addan da ake nema ruwa...

‘Yan sanda sun sami nasarar halaka ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a jihar katsina

‘Yan sanda sun sami nasarar halaka ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a jihar katsina,
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP GAMBO ISAH, ANIPR ya fita a madadin kwamishinan ‘yan sanda jihar, sanarwa tace ‘yan ta’addan sun hadar da Na-Iraqi, Na-Masari.
Sanarwa mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Disambar 2022 tace da misalin karfe 7:30 jami’an ‘yansan sun sami kiran cewa ‘yan bindiga sun tasamma yankin Sokoto – Rima Quarters dake karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina suna harbi kan mai uwa da wabi da bindiga kirar AK47, da nufin yin garkuwa da wani mazaunin yankin.
Babu bata lokaci dakarun dake lura da yankin suka garzaya wurin domin kai dauki, da isar su suka fara musayar wuta da ‘yan bindigar suka kuma sami nasarar hallaka 2 daga cikin su wadanda kuma suna jadawalin wadanda ake nema ruwa a jallo da suka hadar da Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari suka kuma sami nasarar kwato bindiga kirar AK47.
Jami’an ‘Yan sanda sun shiga bincike domin gano wadan suka tsere da raunukan harbi a jikin su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp