Babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yanke wa Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.
An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.
Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin wa’azinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano.
Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya dage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.
Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.
Sai dai kafin a tafi hutun Abduljabar Nasiru Kabara ya bayyana cewa bai san lauyan dake kare shi ba lauyan da ke kareshi ba don haka baya neman afuwa saboda ai cewarsa bai aikata laifi ba, don haka a gaggauta yanke masa hukunci.
Idan za’a iya tunawa A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 8 hours 27 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 9 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com