Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Imo da ke kudancin kasar, ta yi watsi da rahotannin da wasu kafafofin yada labarai a kasar ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan kotun majistire a jihar tare da banka ma ta wuta.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwar da kakakin rundunar ya fitar, inda ya ce wannan labari bashi da tushe bare makama, ta kuma yi mamaki da samu labarin hakan.
Read Also:
Ya bayyana cewa wutar lantarki ce ta janyo tashin gobara a kotun Majistare din, an kuma yi nasarar kashe ta ba tare da bata lokaci ba bisa agajin jami’an kashe gobara da jami’an tsaro.
An kuma killace harabar kotun da baza jami’an tsaro domin tabbtar da babu wanda ya shiga ciki, an kuma fara gudanar da bincike domin gano bakin zaren.
Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da wasu mahara na daban suka kai farmaki kan wata al’umma cikin Enugu wanda yayi sanadin mutuwar mutane da dama.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 52 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 34 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com