Home General Bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara: FRSC zata girke jami’ai sama da  Dubu ...

Bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara: FRSC zata girke jami’ai sama da  Dubu  36 a Sassa Nijeriya

Bikin Kirsimati da Sabuwar Shekara: FRSC zata girke jami’ai sama da  Dubu  36 a Sassa Nijeriya

Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya FRSC, ta sanar da aike jami’anta a sassa daban-daban na kasar domin gudanar da sintiri a tituna yayin gudanar da bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara da ke tafe.

Wannan na cikin jawabin da mukaddashin shugaban hukumar , Dauda Biu ya yi a yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Litinin, ya ce sun tanadi  jami’ai 36,224 da za su yi wannan aikin.

Sai dai ya ce hukumar na bai wa ‘yan Najeriya tabbacin kare lafiyarsu da dukiya a lokacin da ake gudanar da bukukuwan na  karshen shekarar 2022 lafiya da fatan ganin 2023 da ke tafe.

A Najeriya dai ana yawan samun hadurran motoci a manya da kananan titunan kasar, musamman lokacin bukukuwan karshen shekara.

Hukumar kiyaye hadurra ta kasar da ‘yan sanda na dora alhakin hadurran ababen hawan kan tukin ganganci, ko gudu fiye da kima da direbobi ke yi, sai kuma rashin hakurin masu ababen hawa a lokacin da aka samu cunkoun ababen hawa.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp