Home General An Gano Gawarwakin mutane sama da 200 Bayan Gumurzun da akayi da...

An Gano Gawarwakin mutane sama da 200 Bayan Gumurzun da akayi da ‘yan bindiga a jihar Zamfara

An gano gawawwaki 213 da suka hada da ‘yan ta’adda da masu kai musu bayanai, kwanaki kadan da mummunar musayar wutar da aka yi tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan bindigar a wasu yankunan jihar Zamfara.

PRNigeria ta rawaito, sojoji 10 na daga cikin wadanda suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka fantsama garuruwan da ke kusa.

idan za’a iya tunawa a  ranar Litinin PRNigeria ta rawaito dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun yi nasara kan ‘yan bindigar a kauyen Malele da ke karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara.

Samame ta sama da sojojin sama na Najeriyar suka kai a ranar Asabar ya yi nasarar hallaka gwamman ‘yan fashin dajin ciki har da wasu manya daga cikinsu.

An samu karuwar hare-haren ‘yan ta’adda a jihar Zamfara, sakamakon yadda sojojin Najeriya ke fatattakarsu daga inda suke buya, samamen da aka kai garuruwan Malele, Maigoge, Yan Sawayu, Ruwan Tofa, Mai Awaki, and Zama Lafiya, da ke karkashin gundumar Mutunji a karamar hukumar Dansadau sun kara kai mi.

‘Yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar barazana a jihar Zamfara, inda suke haddasa rasa rayuka da dukiya, ko da yake gwamnatin jihar da jami’an tsaro na cewa su na bakin kokarin magance matsalar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp