‘Yan bindiga sun sake hallaka mutane 14, tare da yin garkuwa da 18 a jihohin Sokoto da Katsina dake arewa maso yammacin Nijeriya.
A gabashin jihar Sokoto , an hallaka mutane 13 tare da yin garkuwa da 73 wanda suka hadar da mata da kananan yara.
Hare-haren ya auku a kauyuka mabanbamta, da suka hadar da sabon birni, gada da kuma yankunan karamar hukumar Goronyo.
Jaridar daily ta ruwato cewa an dukkan hare-haren an kai su ne a lokaci gusa ranar litinin din makoon daya gabata.
Da yake tattaunawa da jaridar wani mai rike da sarautar gargajiya a sabon birin, wanda ya bukaci a sakaye sunan sa, ya ce kauyuka 3 mayakan suka kaiwa hari a karamar hukumar sa inda suka hallaka mutane 11.
Kauyukan sun hadar da gatawa da Dangari inda mutane 6 suka mutu, 2 a gatawa 3 kuma a kurawa.
Read Also:
Shugaban jami’an sa kai na Vijilanti a sabonda birni, Musa Muhammad da Dan Majalisa ma wakiltar sabon birnin a zauren majalisar wakilai Mustapha Boza, dake wakiltar Sabon birni ta kudu su bayyana cewa dukkan mutanen an halaka su ne a gona ranar litinin da karfe 5 na yamma.
Boza yace sun kuma yi garkuwa da mutane da dama yayi da suka kai harin.
Haka kuma shugaban karamar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, wand aya koka bisa harin yace maharani sun hallaka mutane 23, yayin da suka yi garkuwa da sauran a garuruwan shinkafi da kagara a ranar litinin din data gabata.
shima Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gada ta gabas a zauren majalisar jiha, Kabiru dauda, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 50 da suka hadar da mata da kananan yara a ranar litinin a yankin.
“bazan iya fada maka takamaiman adadin mutanen da aka sace ba, amma da yawan mutanen mun sun samin raukana, amma dai suka samun kulawar likitoci a asibitocin daban-daban. Kamar yadda ya bayyana.
Dauda ya hakikance cewa duk da korafe-korafen da Al’ummar ke yi bisa harin rashin tsaron da suke ciki, kawo yanzu babu wani matakin da aka dauka domin magance matsalar ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 27 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 18 hours 8 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com