Hatsarin jirgin ƙasa ya kashe aƙalla mutum uku a Legas

An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum uku, yayin da wasu da dama suka samu rauni lokacin da jirgin ƙasa ya buge wata motar bas da safiyar Alhamis a yankin Ikeja da ke jihar Legas.

Shugaban Hukumar agajin gaggauwa ta ƙasa (NEMA), na yankin kudu maso yammacin Najeriya, Ibrahim Farinloye shi ne ya tabbatar da lamarin.

A baya jami’in ya ce mutum biyu ne, sai dai daga bisani ya ce yawan waɗanda suka mutu ɗin ya ƙaru zuwa uku.

Ya ce “mata biyu ma’aikatan gwamnatin jiha da wani namiji ne suka rasu.”

Motar bas ɗin wadda ta gwamnatin jiha ce na ƙoƙarin tsallaka hanyar jirgin ƙasa ta PWD/Sogunle ne a lokacin da jirgin, wanda ya fito daga Abeokuta zuwa cikin birnin Legas ya yi awon-gaba da ita.

Mai magana da yawun Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, Adebayo Taofiq shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ana dai ci gaba da aikin ceto, domin tabbatar da cewa babu sauran wanda abin ya rutsa da shi a maƙale.

Mutane sun rinƙa yaɗa hotunan da suka fito daga wurin da haɗarin ya faru.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 17 hours 55 minutes 15 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 36 minutes 40 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com