Home Labarai Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe masunta 37 a jihar Borno

Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe masunta 37 a jihar Borno

Rahotannin na bayyana cewa mayakan kungiyar ISWAP sun kashe masunta 37 a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya yayin wani hari da suka kai kansu lokacin da suke tsaka da aiki.

Jagoran mayakan sa kai na jihar Borno Babakura Kolo ya shaidawa AFP cewa ‘yan ta’addan sun farmaki Masuntan ne da ke aikin kamun kifi a wajen kauyen Guggo mai tazarar kilomita 18 daga garin Dikwa tare da kasha mutane 37 ta hanyar harbinsu da kuma jefa gawarwakinsu a ruwa.

Majiyoyi daga yankin sun tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na AFP yau alhamis cewa a baya-bayan nan mayakan na ISWAP da takwarorinsu Boko Haram sun tsananta kai hare-hare kan kauyukan jihar ta Borno don satar kayakin abinci.

Mayakan sa kai da ke taimakawa dakarun Sojin Najeriya wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda a yankin sun ce babu tabbaci kan tsagin da ya kai harin na jiya sai dai an tsamo gawarwakin Masuntan 37 a cikin ruwa jiya laraba.

A cewar mayakan, ana ci gaba da laluben gawarwaki a cikin ruwan da kuma cikin dazuka lura da yadda har yanzu aka gaza gano wasu daga cikin Masuntan da suka yi batan dabo.

Rahotanni sun ce mayakan kungiyoyin ‘yan ta’addan na ISWAP da Boko Haram na zargin mazauna kauyukan ko kuma masuntan da sauran manoma da aikin leken asiri ga Sojin Najeriya dalilin da ya sanya kai musu hari.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp