Home Labarai LP ta hade da PDP a jihar Katsina

LP ta hade da PDP a jihar Katsina

Shuwagabannin jam’iyyar Labour Party (LP) reshen jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya sun amince da marawa dan takarar gwamna karkashin inuwa jam’iyyar PDP a jihar, Sanata Yakubu Dan-marke.

Wakilan jam’iyyar bisa jagorancin mukaddashin shugaban jam’iyyar LP ta jihar, Kwamared Mannir Salisu ya jagoranta, ya ce matakin nasu na zuwa ne bayan shugaban jam’iyyar kuma dan takarar kujerar gwamnan jihar ya dangwarar da shahadar jami’yyar LP zuwa Jam’iyyar APC

A cewar Salisu, ’yan takarar da aka zabo daga unguwanni daban-daban, kananan hukumomi da Jihohi, sun cimma wannan matsayar ne bayan kammala shawarwarin da suka dace da nufin neman sahihin dan takara da zai kai jihar ga tudun mun tsira

Salisu yace ‘ya’yan jam’iyyar da suka fito daga mazabu da dama na jihar sun amince da matakin, haka kuma ya bukaci dukkan magoya bayan jam’iyyar Labour Party dake jihar ta katsina su yi fitar farin dango a ranar 18 ga watan maris su kada kur’aun su ga Jam’iyyar PDP mai alamar laima.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp