INEC tace ta shawo kan matsalon data fuskanta a zaben shugaban kasa

Hukumar Zaben Nijeriya INEC ta ce ta gyara dukkan matsalolin da ta fuskanta a yayin zaben Shugaban Kasa da na ’Yan Majalisun Tarayya gabanin zaben Gwamnonin da za a yi a karshen makon nan.

Kwamishinan Hukumar mai kula da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.

Ya ce INEC ta koyi muhimman darussa, kuma za ta yi amfani da su wajen gyara matsalolin da za a iya fuskanta a zaben na Gwamnoni.

Festus ya kuma ce sun yi iya bakin kokarinsu wajen tabbatar da an magance matsalar sashen duba sakamakon zabe na shafin hukumar, wanda aka fi sani da IReV.

Ya ce yanzu haka sashen yada labaran hukumar ya yi shirin ko ta kwana, ko da za a fuskanci kalubale yayin dora sakamakon zabe daga rumfunan zabe a shafin.

Ko a makon da ya gabata, sai da Kotun Daukaka Kara ta amince wa hukumar INEC da ta sake sabunta bayanan da ke kan na’urar tantance masu zabe ta BVAS gabanin zaben na karshen mako.

Sai dai daga bisani INEC ta sanar da dage zaben zuwa ranar 18 ga watan Maris, a maimakon 11 ga wata don samun damar sabunta bayanan.

A wani labarin kuma, Kwamishinan ya ce sama da rumfunan zabe 170,000 ne aka dora sakamakon zaben Shugaban Kasarsu da na Majalisar Tarayya a shafin na INEC.

Ya kuma ce sake sabunta bayanan BVAS din zai kammala ranar Talatar nan, a wani bangare na ci gaba da shirye-shiryen zaben.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 7 hours 24 minutes 54 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 9 hours 6 minutes 19 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com