Home Labarai NSCDC ta dauki sabbin matakan tsaro gabanin zaben Gwamnoni

NSCDC ta dauki sabbin matakan tsaro gabanin zaben Gwamnoni

Biyo bayan Nazari gami da rahotannin da suka biyo bayan zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya a Nijeriya a ranar 25 ga watan Fabreru 2023, hukumar tsaro ta  Civil Defence ta tabbatar da tsarin inganta tsaro domin samun nasarar zaben gamnoni da ‘yan majalisun jihohin mai zuwa.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar Olusola Odumosu ya fitar aka kuma raba ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

An tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da cewa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC sun sami tsaro a lokacin zaben.

Babban kwamandan rundunar Dr. Ahmad Abubakar Audi MNI, OFR ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki kan zaben gwamnonin da ‘yan majalisun jiha, inda yace sun dauk matakin ne domin magance sake samun matsaloli a inda aka samu da kuma magance faruwar hakan a zabukan dake zuwa.

Ya tabbatar da cewa tuni aka tura jami’ai dubu 102, wadanda aka horar da su yadda ya kamata akan yadda zasu tafikas da yamutsi a taron al’umma yadda ya kamata, sarrafa jama’a da dabarun gudanar da zabe domin tabbatar da tsaro.

Ya kuma tabbatar da cewa jami’an zasu cigaba da aiki da al’ummar kasar domin karbar bayanan sirri domin shawo kan matsalolin da kaje-kazo yayin gudanar da zabe da bayan zaben.

Daga bisani Audi ya bukaci ma’aikatan zabe dasu tabbatar da sunyi aiki yadda ya kamata bisa doka da oda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp