Babbar jam’iyya adawa ta NNPP a jihar kano ta zargi daraktan DSS da hada baki da gwamnatin APC a jihar domin yin magudin zabe.
Jigo a jam’iyya kuma guda cikin ‘yan takarar sanata a shiyyar kano ta Arewa a zaben shekarar 2023 Dr. Baffa Bichi ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a yammacin ranar laraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Haka kuma jam’iyyar ta zargi hukumar tsaro ta farin kaya da karawa daraktan hukumar wa’adin aiki kasancewar tuni ya zarta lokacin da doka ta tanadawa ma’aikacin gwamnati ya dauka wato dai shekaru yin ritayar sa.
A don haka jam’iyyar ta NNPP ta shirya gudanar da zanga -zangar lumana a ranar Alhamis 16 ga watan Maris 2023 a kan titin Kano Club dake jihar kano.
PRNigeria Hausa












