Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Usaini Mohammed Gumel mai jagorantar harkokin zaɓen da ke gudana a jihar, ta haramta bikin murnar lashe ta hanyar zagaye kan tituna ko makamancin haka wanda ka iya haifar da hargitsi a jihar.
Kwamishinan ya bayyana haka ga manema labarai a yammacin Asabar bayan kammala zagayen da haɗakar rundunonin tsaro da suka gabatar na sa ido bisa yadda dokar Hukumar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin IG Usman Baba Alkali ta ɗora ma kowane kwamishina a faɗin ƙasar a lokacin zaɓen.
Read Also:
CP Gumel ya kuma yaba da yadda jama’a a jihar Kano suka karɓi shawarwari na a yi zaɓe cikin kwanciyar hankali, inda ya ce farkon zagaye da rundunar ta fara da sauran shugabanin jami’an tsaro sun isa wuraren da ake gudanar da zaɓe inda masu zaɓe suka yi farin cikinsu.
“Mun kuma ga ƙananan yara da ba su isa zaɓe ba a cikin guraren zaɓe inda muka ga bai kamata a ce ana barin su ba dan ana iya samu ‘yan sane da yankan aljihu ko kuma wani ɓata-gari ya yi amfani da su wajen tada husuma a lokacin gudanar da zaɓen.
“Ina roƙon jama’ar jihar Kano yadda aka bada haɗin kai wajen kaɗa ƙuri’a, nan ma ina kira da roƙo kan a ƙara bada goyon baya har lokacin da hukumar zaɓe za ta bayyana wanda ya ci zaɓe ya kasance an taya shi murna ta fuskar da ta dace.
Daga ƙarshe, ya yi jan hankali kan duk wanda ya fito murnar lashe zaɓe da manufar cin zarafin wani, ya sani hukuma ba za ta ƙyame shi ba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 41 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com