Home Labarai Gawuna zai je Kotu domin kalubalantar nasarar Abba gida-gida

Gawuna zai je Kotu domin kalubalantar nasarar Abba gida-gida

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ‘dan takarar Jam’iyyar APC a zaben da aka yi ranar Asabar, Dakta Nasir Yusuf Gawuna ya ce, hukumar zabe ta yi kuskure wajen bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar sakamakon soke zaben wasu mazabun da aka yi.

ya bayyana hakan ne Yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce yawan akwatunan da aka soke ya kai ace hukumar zabe ta sake gudanar da zabuka a wuraren kafin gabatar da kammalallen sakamako da kuma sanar da wanda ya ci.

Mataimakin gwamnan ya ce lura da yadda hukumar zaben ta bayyana zaben ‘yan majalisun jihar Kano 16 a matsayin wadanda ba su kammala ba, wato ‘inconclusive’ ya dace ace ta dauki wannan mataki a zaben kujerar gwamnan.

Gawuna ya ce suna da yakinin cewar Allah ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da yake so, saboda haka za su bi matakan da suka dace ta fannin shari’a domin neman hakkinsu.

Mataimakin gwamnan ya jinjina wa mutanen Kano akan irin goyan bayan da suka ba shi, yayin da ya bukaci kwantar da hankali da kuma kauce wa daukar doka a hannu.

Shi ma a nasa jawabi, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya ce dokar zabe ta yi tanadin cewar, idan an soke zabe a wasu mazabun da kan iya shafar kammalalen sakamakon baki daya, ya zama wajibi a koma domin sake gudanar da zabe a wadannan wurare kafin gabatar da kammalallen sakamako.

Ita dai hukumar zabe ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da kuri’u sama da miliyan guda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp