Janar Irabor ya bayyana haka ne a yayin gabatar da wata makala a jami’ar Edo, yana mai cewa, dubu 13 da 360 daga cikin ‘yan Boko Haram din mayaka ne, inda yace dubu 1 da 543 daga cikin tubabbun mayakan na Boko Haram sun kammala zaman gyaran hali a sansanin Mallam Sidi tsakanin 2016 zuwa 2022, yayin da dubu 1 da 935 aka sauya musu tunani a sansanin Bulumbuktu.
A cewarsa, sojojin Najeriya sun samu jerin nasarori a yakinsu da mayakan na Boko Haram, tare da kakkabe su daga maboyarsu.
Kodayeke Irabor ya ce, lallai rundunar Operation Safe Corridor ta fuskanci kalubale kala-kala a yayin fafatawa da mayakan na Boko Haram da suka hada da karancin kayayyaki da horo da samun goyon bayan kasa da kasa.
Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a sandaiyar rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, yayin da miliyoyi suka kaurace wa gidajensu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 33 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 14 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com