An samu karin mutane 142 da zazzabin Lassa ya hallaka a Najeriya

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya, ta ce cikin kasa da watanni uku, an samu rahoton mutane 784 da suka kamu da zazzabin Lassa, inda mutum 142 suka mutu a jihohin kasar 23.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo, inda ta ce an samu rahoton mutanen da suka kamu da cutar ne, daga watan Janairun 2023 zuwa yanzu.

Haka kuma an samu rahoton bullar cutar ne a jihohin Edo, Ondo, Ebonyi, Bauchi, Taraba, Benue, Rivers, Plateau, da kuma Nasarawa.

NCDC ta ce a jimilla daga mako na 1 zuwa mako na 11, a 2023, an samu rahoton mutuwar mutane 142 daidai da kashi 18.1 cikin 100 wanda ya yi kasa da kashi 18.7 na shekarar 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com