Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International ta ce an samu ƙaruwar yunwa da take hakkin bil adama a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka.
A cikin rahoton da ƙungiyar ke fitarwa shekara-shekara ta bayyana irin tasirin tashe-tashen hankula a mafi yawan ƙasashen Afirka kudu da hamadar sahara, inda ta ɗora alhakin hakan kan rashin ingantaccen shugabanci da ƙungiyoyin duniya.
Rahoton ya ce a nahiyar Afirka ‘yan jarida da masu rajin kare hakkin bil adama da ‘yan adawar siyasa na fuskantar danniya a ƙasashe irinsu Kamaru da Ethiopia da Eswatini da Guinea da Mali da Mozambique da Senegal da kuma Zimbabwe.
Haka kuma rahoton ya ce ”an samu mace-macen masu zanga-zanga da ƙungiyar ta alaƙanta da amfani da ƙarfi fiye da kima da jami’an tsaro ke yi wa masu zanga-zanga a ƙasashen Najeriya da Chadi da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo da Guinea da Kenya da Senegal da Sierra Leone da Somalia da Sudan, da wasu ƙasashe.”
Read Also:
Amnesty International ta kuma nuna cewa rashin hukunta masu take haƙƙin bil adama ya ƙara rura rikice-rikice awasu ƙasashen Afirka.
Rahoton ya kuma ambato raunin ƙungiyoyin duniya ciki har da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyar Tarayyar Afirka wajen kasa magance laifukan take haƙƙin bil adama da aka aikata ƙarƙashin dokokin duniya a ƙasashe irin su Myanmar da Yemen,da wasu ƙasashen nahiyar Afirka da suka haɗar da Ethiopia da Burkina Faso da kuma Sudan ta Kudu.
”Rikice-rikice, da ƙarancin abinci – wanda yaƙin Ukraine ya haddasa da ɗumamayar yanayi – sun kawo cikas wajen yunƙurin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasashen duniya da annobar korona ta haddasa”, in ji rahoton
Kan haka ne rahoton ya ce an take ‘yancin miliyoyin mutane na samun abinci, da lafiya da samun ingantacciyar rayuwa a faɗin ƙasashen Africa.
Domin kuwa a cewar rahoton”mamayar da Rahsa ke yi wa Ukraine ta kawo nakasu wajen samun alkama a mafi yawan ƙasashen Afirka da suka dogara da alkamar ƙasashen biyu.
Sannan tashin farashin makamashi ya haddasa tashin farashin kayan abinci a ƙasashen na Afirka, kamar yadda rahoton ya bayyana
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 7 minutes 15 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 48 minutes 40 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com