Gwamnatin Kano ta yi kira ga zababben gwamnan jihar Engr Abba Kabir Yusuf ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama’a.
A cewarta, irin wannan shawara za ta iya haddasa ruɗani na babu gaira babu dalili a cikin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar don maida martani ga ofishin zaɓaɓɓen gwamnan a kan sanarwar dake cewa duk wasu masu gine-gine a filayen gwamnatin jihar da su dakata nan take.
Read Also:
Gwamnatin Kano ta ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, daidai lokacin da gwamna mai ci har yanzu yake kan mulki, tamkar riga mallam masallaci ne.
Ta ƙara da cewa kamar yadda yake ƙunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba dazama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.
idan dai za’a iya tunawa ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamisa gwamnan mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya fitar da wata sanarwa wadda ya bayyana a matsayin shawara, yana kira ga masu gine-gine a filaye da wuraren gwamnati, ciki har da masallatai da maƙabartu da makarantu da sauransu, su dakata.
Lamarin da ya janyo zazzafar muhawara da ka-ce-na-ce musamman a shafukan sada zumunta.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 45 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 26 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com