Home Labarai Rundunar Yan sanda a Kano sun kama mutum 14 da zargin aikata...

Rundunar Yan sanda a Kano sun kama mutum 14 da zargin aikata fashi da dabanci

Rundunar Yan sanda a jihar Kano ta sanar da kama mutum 14 waɗanda take zargi da aikata fashi da makami da ta’ammali da ƙwayoyi da kuma aikata dabanci a makon farko na watan azumin Ramadan.

Rundunar ta ce an samu nasarar kama mutanen ne a wani samamen da rundunarta ta dawo da zaman lafiya ta kaddamar.

Ta ce ta kuma ƙwato muggan maƙamai da haramtattun ƙwayoyi da kuma kayayyaki da aka sata.

A wata sanarwa da kakakin runduar ƴan sanda jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda ya ayyana yaki kan duk wani nau’i na aikin dabanci a faɗin jihar.

Ƴan sandan sun ce suna iyaƙar kokarinsu wajen dakile dukkan ayyukan ɓata-gari a jihar.

CP Mamman Dauda ya gargaɗi duk masu aikata laifi da su guji yin hakan saboda za su iya fuskantar hukunci mai tsanani idan aka kama su.

Ya kuma bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba, su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp