Home Labarai NBC ta ci tarar Tashar Channels Miliyan 5

NBC ta ci tarar Tashar Channels Miliyan 5

Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya NBC tace tarar kafar yada labari ta Channels TV bisa wata tattaunawa da tayi da wanda ya yi wa Jam’iyyar LP takarar mataimakin shugaban kasa a kakar zaben shekarar 2023 Baba-Ahmed.

Ta cikin Shirin Politics Today na makon daya gabata Baba-Ahmed ya bukaci babban Alkalin alkalan Nijeriya Olukayode Ariwoola da kada ya rantsar da Bola tinubu matsayin shugaban kasa.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar na Jam’iyyar LP yace babu zababben shugaban kasa saboda Tinubu bai cika ka’idojin tsarin Mulki ba.

Kamfanin dillancin labaru na Nijeriya NAN ya rawaito cewa tarar na cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 27 mai dauke da adreshin baban daraktan tashar  na Channels.

shugaban hukumar ta NBC yace za ta iya tunzura jama’a tare da kawo hargitsi a ƙasar, don haka a cewar hukumar, ta saɓa wa dokokin yaɗa labarai.

lllelah ya ci gaba da cewa a lokuta da dama, hukumarsa ta sha faɗa wa gidan talabijin ɗin ya riƙa la’akari da zaman lafiyar ƙasar, kafin yaɗa kowanne irin shiri nasa.

Don haka ya ce hukumar ta sanya wa gidan talbijin ɗin tarar naira miliyan biyar a kan wannan saɓa ƙa’ida, tare da gargaɗin Channels TV ya kiyaye aukuwar irin hakan a nan gaba.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp