Home Labarai Yan bindiga sun yi garkuwa da Yara sama da 80 a ...

Yan bindiga sun yi garkuwa da Yara sama da 80 a jiharZamfara

wasu rahotanni daga karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da sama da mutane 80 ne a ranar Juma’a.

Mutanen da lamarin ya ritsa da su daga yankin, bayan isar su daji wajen neman itace da safiyar juma’a, sai labarin sace wasu daga cikin mutanen yankin daga yan bindiga ya kuno kai, a dai dai lokacin da wasu ke cikin aiki a gonakinsu.

Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara mai suna Sani Wanzamai ya ce an yi garkuwa da yara kusan 80 daga kauyen Wanzamai tare da wasu fiye da 20 daga kauyen Kucheri da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar da kuma al’ummar Yankara a makwabciyar Katsina. an kuma sace jihar.

Ana sa ran yawan mutanen da yan bindigar suka yi garkuwa da su tsakanin 80 zuwa 100, yawancinsu matasa ne tsakanin shekarun 15-18 da wadanda suka kai shekaru ashirin. Akwai wani dattijo wanda shekarunsa hamsin ne. Sai dai yawancin wandada aka yi awon gaba da su matasa maza da mata ne.

Ya zuwa wannan lokaci ana dakon sanarwa daga rundunar tsaro domin tabbatar da aukuwar wannan al’amari.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp