Gwamnatin Najeriya ta amince a kashe naira biliyan 250 a bana, a shirinta na rage talauci da take gudanarwa a faɗin ƙasar.
Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya yi kan rahoton ci gaban da aka samu a shirin rage talaucin na ƙasa da ake kira NPRGS a gaban kwamitin da ya jagoranta ranar Laraba.
Ayyukan da aka tsara aiwatarwa a 2023 ƙarƙashin shirin NPRGS sun haɗa da: “Gina gidaje dubu ɗari ga masu ƙaramin ƙarfi, aikin da zai samar da ayyukan yi miliyan ɗaya na kai-tsaye ko a kaikaice.
“Faɗaɗa samun makamashi ta hanyar samar da fitilun gefen titi 1,200 a yankunan karkara da kuma wasu ƙananan tashoshin lantarki da za a riƙa amfani da su a gonaki ƙarƙashin wani shiri mai suna Solar Naija.
“Samar da ayyuka miliyan huɗu da ɗari biyar na kai-tsaye ko kuma a kaikaice ta hanyar shirin gina hanyoyi a yankin karkara da za su haɗa kasuwannin ƙauye 750 a faɗin Najeriya.
Read Also:
“Samar da tallafin naira biliyan tara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi a daminar bana karkashin shirin samar da aikin yi a bangaren noma.
“Fadada rijistar mutanen da ke samun tallafin rayuwa da ƙarin magidanta miliyan uku.”
A lokacin gabatar da bayanin, ministan kasafin kudi da tsare tsare, Clem Agba, ya ce mutum miliyan biyu ne suka amfana da shirin NPRGS kai-tsaye a 2022.
Rahotonsa ya bayyana cewa manoma miliyan daya da dubu 600 ne suka amfana da shirin a karkashin shirin habbaka noma.
Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriyan ya fitar a jiya, ta ce matasa 13,000 ne suka samu horo kan ƙere-ƙere da kuma sana’o’in hannu a jihohi 6 da suka hada da Legas da Ogun da Enugu da Gombe da Kaduna da kuma Nasarawa, yayin da ake shirin samar da irin wannan tsari ga matasa 2,000 a jihar Edo.
Ya ce ‘yan Najeriya fiye da 8,000 aka ɗauka aikin shimfiɗa tituna a yankunan karkara ƙarƙashin shirin samar da hanyoyi a karkara, inda aka gina hanya 40 da suka ratsa kauyuka 120 a faɗin Najeriya.
“A duk faɗin Najeriya mutum 1,818,782 ne suke cin gajiyar shirin NPRGS, kuma an ɗauki mutum 9,527 aiki ƙarƙashin aikin ya zuwa yanzu.”