Home Labarai DSS ta kama ‘yan bindiga a Kano

DSS ta kama ‘yan bindiga a Kano

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya DSS ta ce ta kama wasu ‘yan bindiga biyu dauke da makamai a Jihar Kano da ke arewacin kasar.

wannan na unshe ta cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis,  inda ta ce ta kama mutanen ne yayin da suke kan hanyarsu ta kai makaman wata jiha da zummar kaddamar da hare-hare.

Sanarwar, wadda kakakin DSS, Peter Afunanya ya sanya wa hannu ta kara da cewa an kwace makamai daban-daban daga hannun ‘yan bindigar.

Abubuwan da aka kama sun hada da bindiga kirar AK-47 guda biyu da kwanson harsasai na AK47 shi ma guda biyu da babur guda daya da kuma wani buhun doya da aka boye bindigogi.

“Hakan ya nuna cewa akwai bukatar mutane su lura da kyau sannan su kai rahoto ga jami’an tsaro da ke kusa da su kan duk wani motsi na mutanen da ba su amince da su ba,” a cewar Afunanya.

Hukumar tsaro ta yi kira ga wuraren shakatawa da su sanya ido sosai a lokacin bukukuwan karamar Sallah.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp