Home Labarai Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan Ta’ addan 3 a jihar Zamfar

Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan Ta’ addan 3 a jihar Zamfar

Dakarun sojin Najeriya karkashin Rundunar Operation HADARIN DAJI sun sami asarar hallaka ‘yan bindiga 3 a wani musayar wuta a dajin Gusau.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na shalkwatar rundunar Manjo Janar Musa DANMADAMI.

Sanarwar mai dauke da kwana watan 30 ga wata Afrilu 2023, tace a wani aikin tarwatsa ‘yan bindiga rundunar ta tarwatsa gungun su na Anka ANKA, karkashin ikon DAN KAMFANI dake karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Dakarun sojin sun yi arangama da’ yan bindiga inda suka hallaka 3 daga cikin su, tare da kwato bindiga kirar PKT guda 1, dauke da gidan Alburushi 48 masu tsayi mita 7.62 wanda ke dauke da Alburushin kwaya 54, sai bindiga kirar AK47 guda 3, sai kuma kunson Alburushin na musamman mai tsayi mita 7.62 da kuma baburan hawa 3.

Matakin babban iko na rundunar HADARIN DAJI ya yaba da aikin dakarun sojin, tare da neman Al’ummar gari su cigaba da basu hadin kai domin kakkabe ayyukan ‘yan ta’ addan a yankin.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp