Rundunar ƴan sanda a jihar Kano sun sanar da kama matashin nan Ibrahim Musa da ake zargi ya hallaka mahaifiyarsa a Kano.
A wani sako da kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an kama matashin ne a maɓoyarsa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar ta Kano.
Read Also:
Kiyawa ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma ya ce yana tu’ammali da ƙwayoyi masu sa maye.
A yanzu dai za a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike.
A jiya ne dai aka ruwaito cewa matashin ya caccaka wa mahaifiyarsa mai shekara 50 wuƙa a kanta da ƙirjinta da kuma sauran sassan jiki, inda ya tsere bayan aikata laifin.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1480 days 14 hours 53 minutes 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1462 days 16 hours 34 minutes 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com