Rahotannin na bayyana cewa akalla mutane 20 ne suka mutu sakamakon wani rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilun Wurkunawa da kuma Karimjo a Karamar Hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.
An kuma kona gidaje da dama da asarar dukiya mai dimbin yawa.
Tashin hankalin ya samo asali ne kan batun sarautar gargajiya a yankin.
A cikin makon da ya gabata ne gwamnan jihar ta Taraba Darius Ishaku ya bai wa Alhaji Yakubu Abubakar Haruna sanda a matsayin sabon sarki a masarautar Wurkum da ke Karamar Hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
An nada sarkin ne bayan rasuwar mahaifinsa da ya shafe shekara 47 yana mulki.
Jihar ta Taraba dai na guda cikin jihohin dake fama da rikicin kabilanci, abinda ke haddasa asarar rayuka da tsarin dukiya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 30 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 20 hours 11 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com