Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargadin samun ruwan sama mai karfin gaske gami da tsawa a wasu sassa na arewa maso gabashin Najeriya.
Kakakin hukumar, Muntari Ibrahim ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewarsa, jihohin da za su fuskanci wannan yanayi sun hada da Borno da Adamawa da Gombe da kuma Taraba.
Read Also:
Sannan sanarwar ta kuma ce za a samu ruwa tafe da iska a jihohi irinsu Gombe da Bauchi da Benue da Filato da Nasarawa da Enugu da Ebonyi.
Sai wasu kuma jihohin kudanci. Rahoton ya ce za a shafe tsawon sa’a uku zuwa shida ana tafka ruwan.
Nimet ta shawarci mutane suyi takatsan-tsan da kasancewa masu kula saboda tsaronsu.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 39 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 20 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com