Zababben gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rushe wasu gine gine da aka yi a kewayen filin sukuwa dake unguwar Nassarawa.
Read Also:
Abba Kabir da sauran mukarraban gwamnati Hadi da jami’an tsaro sun Isa wajen ne da misalin karfe 1 da minti 30 na Daren Asabar, Kuma an rushe wasu muhimman sassa na gine-ginen Nan take.
Idan za’a iya tuna tun bayan samun Nasara a zaben gwamnoni na 2023 Gwamnan kanon ya shawarci masu gine gine a filayen gwamnatin jihar dasu dakata.
Sai dai ana kallon wannan aiki kai tsaye wani mataki ne na dawo da dukiyoyin gwamnatin da aka sayar ba bisa ka’ida ba.
PRNigeria hausa