Home Labarai NLC DA TUC sun fasa shiga yajin aiki

NLC DA TUC sun fasa shiga yajin aiki

Rahotannin daga Nijeriya na bayyana cewa Manyan kungiyoyin kwadago biyu a kasar na NLC da TUC sun jingine aniyarsu ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani wanda suka shirya farawa ranar Laraba kan tashin farashin man fetur.

Kungiyoyin biyu sun yanke wannan shawarar ce bayan ganawar da suka yi da bangaren gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa, ranar Litinin.

A makon da ya gabata ne dai kungiyoyin kwadago na Najeriya suka bai wa gwamnatin kasar wa’adin zuwa ranar Talata 6 ga watan Mayu domin ta janye cire tallafin man fetur ko kuma su tsunduma yajin aiki.

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da matsayar, wadda shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, Joe Ajero ya tabbatar, bayan kwashe kimanin sa’oi shida ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

Wata sanarwar da shugabannin NLC da TUC suka sanyawa hannu, ta ce daya daga cikin dalilan jingine yajin aikin shi ne bai wa gwamnatin tarayya da bangaren ‘yan kwadago damar kafa wani kwamiti da zai duba batun yin karin albashin ma’aikata da kuma lokacin da za a aiwatar da tsarin.

Haka nan kuma za a duba tsarin bayar da tallafin kudade na Bankin Duniya ta yadda za a sanya masu karanin karfi a ciki.

Daga nan kungiyar kwadagon da gwamnati za su sake duba tsarin gyaran matatun man fetur na kasar ta yadda za a iya kammala gyara su.

Bugu da kari gwamnati za ta samar da tsarin gyara hanyoyin mota da kuma samar da layukan dogo a fadin kasar.

A karshe sanarwar ta ce kungiyar kwadago za ta sake yin wani zama da gwamnatin tarayya a ranar 19 ga watan Yuni domin samar da matsaya kan yadda za a aiwatar da tsare-tsaren da aka cimma.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp