Gwamnatin Kano zata tabbatar da an aiwatar tare da kammala duk wasu ayyuka da hukumomi masu bada tallafi na kasashen duniya ke aiwatarwa a Kano.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf, ta jaddada kudirinta na bibiyar duk wasu ayyuka da bankin duniya da sauran hukumomi masu bada tallafi ke aiwatarwa a Kano.
Tabbacin hakan ya fito ne ta bakin babban Akanta na Kano Abdulkadir Abdussalam lokacin da yake jagorantar wata ganawa da wakilan kungiyoyi da hukumomin kasashen waje wadanda ke bada tallafi.
Ganawar dai ta hada da dukkanin akantoci dake jihar da kuma masu lura da hukumomin gwamnati.
Read Also:
Abdussalam, ya nuna damuwarsa akan yadda wasu daga cikin ayyukan aka gaza kammalasu wanda hakan ya kawo koma baya a cigaban tattalin arzikin Kano.
Babban Akantan ya buga misali da bangarori irinsu ruwansha da ilimi da lafiya da kuma noma, da yadda kuma suke da alaka takai tsaye da gina dan Adam.
A karshen ganawar, Abdulkadir Abdussalam ya baiwa masu ruwa da tsakin tabbacin gwamnatin Kano na tsayawa tsayin daka domin amfani da tallafin dake shigowa Kano ta hanyar data dace.
Amakon daya gabatane dai Gwamna Abba Kabir Yusuf yanada Abdulkadir Abdussalam amatsayin sabon babban Akantan Kano, kafin nadin nashi dai Darakta ne a hukumar tattara haraji ta jihar Kano.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 5 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 46 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com