Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a ranar alhamis zuwa Faransa domin halartar wani taron musamman kan sabuwar yarjejeniyar hada hadar kudade ta duniya.
Taron na kwanaki biyu, zai maida hankali ne kan yadda za’a fitar da sabbin dabaru musamman ga kasashen dake fuskantar matsalolin kasafin kudi na gajeren zango.
Mashawarci na musamman ga shugaban kasar kan harkokin sadarwa shine ya bayyana batun balaguron shugaban kasar a wani jawabi daya fitar a ranar litinin.
Wannan ne dai karon farko da shugaban zai bar Najeriya a hukumance domin halartar wani taro a kasashen waje.
PRNigeria hausa