Home Labarai Kwashe Shara na Kara fito da martabar Kano – Danzago

Kwashe Shara na Kara fito da martabar Kano – Danzago

Gwamnatin jihar Kano ta ce kwashe sharar dake jibge akan titin gidan sarkin Kano daura da gidan Dan masani dab da Kofar shiga Makarantar SAS a matsayin Wani muhimmin aiki Wanda zai Kara fito da martabar Kano.

Shugaban kwamitin karta kwana na kwashe sharar jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago shine ya bayyana hakan a alhamis dinnan lokacin da jami’an hukumar kwashe shara ta jihar suka yi dirar mikiya a wajen domin gabatar da ayyukansu.

A cewar Dan zago hanyar zuwa gidan Dan masani da Kofar shiga Makarantar S.A.S wurare ne masu matukar amfani da tarihi ga al’ummar Kano, a don haka akwai bukatar Samar da kyakkyawan yanayi a wuraren domin samun cikakkiyar tsafta.

Dan zago daga nan sai ya bukaci al’ummar dake rayuwa a yankunan dasu kasance masu bin doka da oda ta hanyar Kai sharar su wuraren da hukuma ta tanada domin zubarwa, wanda hakan zai samar musu da ingantacciyar rayuwa me cike da lafiya da tsafta.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp