Gwamnatin Jihar Kano ta kare matakin da ta dauka na rushe wasu Gine Gine da tayi a Birnin Kano.
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf shine ya Bayyana Hakan Yayin da ya karbi Bakuncin sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a safiyar Juma’a a Gidan Gwamnatin Jihar yayin Bikin Hawan Nasarawa.
Read Also:
Gwamnan yace rushe Gine Ginen masallacin Idi jihadi ne Kuma an Kara kima da martaba ga masarautar ta Kano
Shima a nasa jawabin Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace masarautar ta Kano zata Cigaba da Baiwa Gwamnatin Jihar Kano Hadin Kai da Goyon baya Domin Sanarwa al’umma cigaba.
PRNigeria hausa