Ƙungiyar Ƙwadago na shirin tsunduma yajin aiki a duk faɗin Najeriya wanda zai fara ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023.
Read Also:
Duk da umarnin kotun da ya dakatar da ƙungiyar daga shiga yajin aiki a watan Yunin da ya gabata yana nan, an fahimci cewa, ƙungiyar ta nuna ba zata naɗe hannunta ba bayan ƴan Najeriya suna ci gaba da shan azaba saboda janye tallafin mai.
A watan Yunin da ya gabata ne dai gwamnatin Tinubu ta kai haɗaɗdiyar ƙungiyar ƙwadagon kotu domin ta haramta mata shiga yajin aikin gama-gari biyo bayan janye tallafin man fetur.
PRNigeria hausa