Home Labarai Bazoum ya magantu bayan Juyin Mulki a Nijar

Bazoum ya magantu bayan Juyin Mulki a Nijar

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya yi amfani da kafar sada zumunta ta yanar gizo a ranar alhamis din nan tare da shan alwashin kare dimokiradiyya kwana guda bayan hambarar da shi a wani juyin mulkin da sojoji suka yi.

Ministan harkokin wajen kasar Hassoumi Massoudou shi ma ya fitar da wani rubutu a dandalin X, wanda aka fi sani da Twitter, domin “dukkan masu ra’ayin dimokaradiyya da masu kishin kasa” su sa juyin mulkin ya gaza.

Bayanin nasu ya biyo bayan wani jawabi ne da sojoji suka yi daren ranar Laraba a gidan talabijin na kasar.

Inda suka sanar da cewa an cire Bazoum daga kan karagar mulki tare da dakatar da dukkan hukumomin jamhuriyar, wanda ke zama juyin mulki karo na bakwai a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka tun shekara ta 2020.

A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka datse fadar shugaban kasar da ke Yamai babban birnin kasar tare da tare Bazoum a ciki.

Wannan ya haifar da damuwa a yanki da na duniya game da rashin zaman lafiya a kasar da ke zama babbar abokiyar kawance ga kasashen yammacin Turai da ke taimakawa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Har yanzu ana tsare da Bazoum a cikin fadar shugaban kasa da safiyar Alhamis din nan, Massoudou ya fada a wata hira da kafar yada labaran Faransa ta France 24. Ba a san inda ministan yake ba.

Yamai shiru da sanyin safiyar Alhamis din nan yayin da ‘yan kasar suka farka da rufe kan iyakokin kasar da dokar hana fita da sojoji suka kafa a fadin kasar

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp