Wata babbar kotu a Abuja ta yi watsi da buƙatar da hukumar DSS ta gabatar mata mai neman izinin ci gaba da tsare dakataccen babban bankin Najeriya, Godwin Emefile da kwanaki 14 a bisa ƙarin shaidun da tace ta tattara a kan shi.
Mai shari’a Hamza Muazu ya yi wasi da ƙarar, yana kafa hujja da saɓawa zaman kotu, tare da bayyana cewa kotun bata da hurumin sauraron buƙatar.
Read Also:
A ranar Talata, an samu jayayya tsakanin jami’an DSS da na hukumar kula da gidan gyaran hali ta Najeriya a kan wanda zai ci gaba da tsare Mr Emefiele bayan kotu ta bayar da belinsa.
DSS ta yi Allah-wadai da lamarin, kuma ta sha alwashin gudanar da bincike a kai.
Ita dai DSS tana zargin Emefiele da laifin mallakar bindiga da harsashi ba bisa ƙa’ida ba, zargin da kuma ya musanta.
Za a ci gaba da shari’arsa ne a ranar 14 ga watan Nuwamba.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 5 hours 14 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 6 hours 55 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com