Home Labarai Tinubu ya kaddamar da matakan inganta tattalin arzikin

Tinubu ya kaddamar da matakan inganta tattalin arzikin

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaddamar da wasu matakai daban daban da za su zaburar da tattalin arzikin kasar da zummar shawo kan kuncin rayuwar da jama’ar kasar suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur.

‘yan tsiraru kawai ke amfana da shi, yayin da akasarin jama’ar kasar ke shan wahala.

Shugaban ya ce a cikin watanni biyu da suka yi a karagar mulki, gwamnatin sa ta yi nasarar ceto sama da naira triliyan guda daga cikin makudan kudaden da ake zubawa a matsayin tallafin man, wadanda za’a karkatu su wajen bunkasa harkar ilimi da harkokin kula da lafiya da kuma samar da kayan more rayuwa.

Tinubu wanda ya ce ya fahimci halin kuncin da ‘yan Najeriya suke ciki, ya kuma bayyana shirye shirye da dama da gwamnatin sa za ta aiwatar wajen samar da rance ga masu kanana da matsakaitan masana’antu domin bunkasa harkokin su ta yadda za su amfana ta hanyar biyan kashi 9 na kudin ruwa.

Shugaban ya kuma jinjinawa masu kamfanoni da masana’antu saboda dagewar da su ke da ita wajen ci gaba da harkokin su a cikin irin wannan yanayi mai tsauri.

Shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa na tattaunawa da kungiyoyin kwadago da zummar kara albashin ma’aikata saboda tinkarar halin da ake ciki, yayin da kuma ya ce zai aiwatar da shirin sa da ya yi alkawari na tallafawa marasa karfi a cikin al’umma

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp