Kungiyoyin kwadago sun janye zanga zangar da suka fara gudanarwa a sassan Nijeriya.
Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da shugabancin kungiyar yayi da shugaban kasar Bola Tinubu a fadar sa dake birnin tarayya Abuja.
Kungiyoyin kwadago da suka hadar da NLC da TUC sun amince da dage zanga zangar ne biyo bayan muhimmiyar tattaunawa da suka yi da shugaban.
Read Also:
Shugabancin kungiyoyin ya nuna ganuwarsa bisa karin gwiwar Shugaba Tinubu na daukar matakin magance matsalolin da suka addabi ma’akatanka da Al’ummar kasar.
Tinubu ya tabbatar da cewa matata mai ta Fatakwal zata dawo aiki ka’in da na’in domin inganta tattalin arzikin kasar.
Ta cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman da sadarwa Dele Alake ya fitar ta tabbatar da janyewar zanga zangar kungiyar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 4 minutes 33 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 45 minutes 58 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com