Home DUNIYA RFI da France 24 sun yi tur da rufe tashoshinsu a Nijar

RFI da France 24 sun yi tur da rufe tashoshinsu a Nijar

Gidan rediyon RFI da gidan talabijin na France 24 sun yi Allah-wadai da matakin da hukumomin sojin Nijar suka dauka na dakatar da su daga yada shirye-shiryensu a kasar, mako guda da juyin mulkin da sojojin suka yi a kasar.

Hukumar Gudanarwa kafofin yada Faransa a kasashen ketare ta France Medias Monde ta bayyana matakin a matsayin wanda ya yi hannun riga da dokokin shari’a, lamarin da ta ce zai dakile wa ‘yan kasar hanyoyin da suke samun cikakkun labarai cikin ‘yanci.

Wannan na zuwa ne bayan irin wannan dakatarwar da sojojin da ke mulki a Mali da Burkina Faso suka yi wa RFI da France 24 a watannin da suka shude.

Hukumar ta France Medias Monde ta jaddada kudirinta ga ‘yancin yada labarai da kuma kare lafiyar ‘yan jaridarta.

RFI na yada shirye-shiryensa a tashoshin FM guda bakwai baya ga gajeren zango da sauran hanyoyin tauraron dan adam cikin harsunan Faransanci da Hausa da Fulfulde.

Kazalika akwai wasu karin gidajen rediyo 44, abokan huldar RFI da su ma ke yada shirye-shiryensa cikin harsunan Faransanci da Hausa da Fulfulde a Nijar.

A shekarar 2022, wasu alkaluma da aka tattara sun nuna cewa, kimanin masu saurare miliyan 1 da dubu 900 ne ke sauraren RFI a kowanne mako a kasar ta Nijar, wato kwatankwacin kashi 18 na daukacin al’ummar kasar, yayin da RFI din ke zama kafar yada labarai ta ketare mafi girma a kasar kamar yadda wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna.

Har ila yau, alkaluman sun nuna cewa, kimanin rubu’in daukacin jama’ar Nijar ne suka bibiyar tashar ta RFI a kowanne mako a shekarar bara.

Koda yake har yanzu ana iya samun RFI da France 24 ta hanyoyin tauraron dan adam kai tsaye kamar su Eutelsat da Arab-Sat, sai kuma gajeren zango.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp