Tsohon Babban Kwantirolan hukumar kula da shige da fice na kasa Immigration, Muhammad Babandede, ya shawarci gwamnatin Kano da ta gina kasuwannin da za’ake hada-hadar kasuwanci da cinikayya na tsawon sa’o’i 24 babu yankewa, domin bunkasa tattalin arziqin jihar.
Read Also:
Muhammad Babandede, ya fadi hakan ne lokacin da yake gabatar da wata lakca mai taken rawar da hukumar kula da shige da fice ta kasa Immigration ke takawa wajen habaka kasuwancin jihar Kano, a wani bangare na bikin cikar hukumar shekaru 60 da kafuwa, wacce hukumar lura da shige da ficen reshan jihar Kano ta shirya a dakin taro na Labanon Club dake Unguwar Bompai.
Yace samar da kasuwannin masu ci tsawon awanni 24 a fadin jihar Kano dake zama cibiyar kasuwancin Najeriya, hakan zai taimaka matuka gaya, wajen samar da tsaro da cire da mummunan tinani a zukatan matasa da kuma bunkasa tattalin arziqin kasa da jiha baki daya.
Daga bisani Tsohon Babban Kwantirolan hukumar kula da shige da ficen na kasa Immigration, Muhammad Babandede, ya bukaci hukumar ta Immigration, reshan jihar Kano dama na sauran jihohin Najeriya da su hada hannu da sarakunan gargajiya don samun nasarar tafiyar da aiyukansu yadda yakamata.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 53 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 34 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com