Shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa reshan jihar Kano, AD Bagari, yace hukumar ta sami tarin nasarari tun bayan kafuwarta a shekarar 1963, bama a jihar kano ba har a kasa baki daya.
AD Bagari ya bayyana hakan ne yayi zantawarsa da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron bikin cika shekaru 60 da kafa hukumar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A cewar sa amfani da hanyoyin zamani wajen hana kwararar baki ba bisa ka’ida ba zuwa kasar nan suma sun taka muhimmiyar rawa waje daga martabar hukumar a kasashen duniya.
PRNigeria ta rawaito cewa, taron ya sami halartar Mai martaba sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero bisa wakilcin malam Lamido Abubakar Bayare Bunun Kano, Sheik Khalil Ahmad Adamawa wakilin masarautar Saudiya da sauran manyan baki daga kasashe makotan Nijeriya da sauran kasashen duniya.
PRNigeria hausa












