Home DUNIYA Kungiyar EU ta taimaka wa INEC da kayan aiki

Kungiyar EU ta taimaka wa INEC da kayan aiki

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta samu kyautar wasu kayan aiki daga ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU, da za su taimaka wajen inganta harkokin zaɓen ƙasar.

Shugabanb hukumar zaɓen ƙasar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, lokacin karɓar kayayyakin a Abuja bban birnin ƙasar.

Farfesa Yakubu ya ce sabbin kayan aikin za su taimaki hukumar zaɓen ƙasar wajen inganta harkokin zaɓenta.

Yav ƙara da cewa akwai wasu ƙarin kayayakin masu yawa da ƙungiyar EU za ta bai wa hukumar tasa.

”Waɗannan kayayyaki za su taimaka wa hukumar zaɓen wajen inganta harkokinta a ɓangarori da dama”, in ji shugaban hukumar.

Kungiyar ta EU dai na daga cikin kungiyoyin da ke sanya idanu a zaɓuklan Najeriya, inda a lokuta da dama, ƙungiyar ke cewa ana tafka kura-kurai a tsarin zaɓukan ƙasar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp