Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya nada Sabbin shuwagabanni hukumomi da ma’aikatun 8 dake karkashin hukumar sadarwa da wayar da kai ta kasar.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mashawarci kan yada labarai ga shugaban kasar Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu a birnin tarayya Abuja.
Sanarwar tace an nada: According to the statement those appointed are:
(1). Mr. Lanre Issa-Onilu matsayin shugaban hukumar wayar da kai ta (NOA)
(2) Mr. Salihu Abdulhamid Dembos matsayin shugaban gidan Talabijin na kasa (NTA).
(3) Dr. Muhammed Bulama matsayin shugaban gidajen Radio Gwamantin Tarayya (FRCN).
Read Also:
(4) Mr. Charles Ebuebu matsayin shugaban hukumar dake lura da kafafen yada labarai na Nijeriya (NBC).
(5) Mr. Jibrin Baba Ndace matsayin shugaban kafar yada labarai ta (VON)
(6) Dr. Lekan Fadolapo shugaban hukumar dake lura da tallace-tallace a kafafen yada labarai ta (ARCON).
(7) Mr. Ali Muhammed Ali matsayin shugaban kamfanin dillancin Labarai na Nijeriya News (NAN).
(8) Mr. Dili Ezughah matsayin shugaban (NPC).
Sanarwa ta bayyana cewa Tinubu ya bukaci sabbin shuwagabannin dasu zama masu amfani da fikira wajen ciyar da inda aka dora musu nauyin lura dashi gaba, tare da jagorori na kwarai.
Ta kuma cewa nadin nasu ya fara aiki nan take.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 49 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 31 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com